Kasar Sweden ta bayyana cewa, ta shirya tsaf domin daukar nauyin gasar yin jima’i a bainar jama’a wadda za a fara a ranar Alhamis.
Gasar wadda mahukuntan suka tsara za a fara gudanarwa a gobe 8 ga watan Yunin 2003, za a shafe kwanaki shida, ana fafatawa.
Wadanda za su shiga cikin gasar, za su fafata a gasar ta jima’i a bainar jama’a da za rinka gudanar da ita a kullum.
Alkalan da za su sanya ido gasar tare da yin la’akari da ra’ayoyin masu kallon gasar, za su tantance wanda ya zai zama zakaran gasar.
Wadanda za su fafata a gasar, za su shafe mintuna 45 zuwa awa daya suna yin lalatar, ya danganta da irin karfin kuzarin wanda zai yi jima’in.
Za a gudanar da gasar ne, a matakai uku don samun maki.
Ana son masu yin gasar su samu makin da ya kai daga 5 zuwa 10, tare da samun kuri’u daga wajen ‘yan kallo da kuma hukunci da alkalan gasar su biyar da za su yanke zakaran gasar.
Daga cikin alamomin da za a yi la’akari da su a yayin aikata masha’ar don fitar da zakara sun hada da, fahimtar hakikanin yadda ake yin jima’a, juriya a lokacin da ake yin jima’in.
Shugaban gasar, Dragan Bratych ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka amince da yin gasar, a matsayin wasa, inda ya ce, hakan zai kara karfin kiwon lafiya ga wadanda suka shiga cikin gasar.
Bratych ya yi nuni da cewa, manufar gasar shi ne, sanya babban jin dadi a tsakanin mace da namjin da za su shiga cikin gasar.
A cewarsa, gamsuwar yin jima’i a tsakanin mace da namji da za su fafata a gasar, ita ce za ta tabbatar da an samu nasara a gasar, amma idan ba samu hakan ba, ba a samu nasara a gasar ba.