Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira ga gwamnatin mulkin Myanmar da ta saki Aung San Suu Kyi yayin da ya amince da kudurinsa na farko kan halin da ake ciki a yankin kudu maso gabashin Asiya mai fama da rikici.
Majalisar mai wakilai 15 ta shafe gwamman shekaru tana fama da rarrabuwar kawuna kan Myanmar kuma daga bayan nan ne ta cimma matsaya a kan rikicin kasar, wacce ke karkashin mulkin soja tun watan Fabrairun 2021, lokacin da aka hambarar da Suu Kyi.
Suu Kyi, mai shekaru 77, ta kasance a tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatinta kusan shekaru biyu da suka gabata tare da murkushe masu adawa da gwamnatin.
Kudirin da kwamitin ya cimma a ranar Laraba, ya bukaci gwamnatin sojin Myanmar ta saki wadanda take tsare da su, ciki har da Suu Kyi da tsohon shugaban kasar, Win Myint.
Ya kuma bukaci kawo karshen dukkannin nau’ikan rikici a kasar ba tare da bata lokaci ba, kana ya roki dukkannin bangarori su mutunta hakkin dan adam.
A wani labarin na daban gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin da Talata 26 da 27 ga watan Disamba 2022 da kuma Litinin 2 ga watan Junairu a matsayin ranakun hutun bukukuwan Kirsimeti da ranar Dambe da sabuwar shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hutun ga ‘Yan Nijeriya a madadin gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, ya muma taya mabiya addinin kirista da sauran ‘yan Nijeriya mazauna gida da na kasashen waje murnar bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ta bana.
Aregbesola ya hori Kiristoci da su yi koyi da Yesu Kiristi a cikin ayyuka da kuma bin koyarwarsa, musamman a kan bin gaskiya da zumunci da ƙaunar juna.
Aregbesola ya kuma tabbatar wa da ‘Yan Nijeriya cewa, gwamnati ta samar da ingantattun matakai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, kuma yana sa ran ‘yan Nijeriya za su tallafa wa kokarin hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu amfani da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance masu lura da tsaro, inda ya bukaci da su kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da basu gamsu da su ba ga hukumar tsaro mafi kusa da su.