Kungiyar super eagles mai wakiltar Najeriya ta sha kashi a hannun Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a karawar da suka yi na neman zuwa gasar cin kofin duniyar da za’ayi a Qatar a shekara mai zuwa.
Namnganda wanda ba a fara wasan da shi ba, ya rufe bakin Yan kallon da suka yi tururuwa zuwa filin wasan Lagos lokacin da ya jefawa kasar kwallon da ya taimaka mata samun nasara.
Wannan nasarar ta baiwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya damar samun maki 3 daga Najeriya da kuma zama a matsayi na 3 a tebur na rukunin Ca da maki 4 kamar yadda Cape Verde ke da maki 4 a matsayi na 2, sai dai har yanzu Najeriya na da maki 6 a matsayi na farko.
Wannan rashin nasara ya yiwa ‘Yan Najeriya masu sha’awar kwallon kafa illa, musamman ganin cewar a Najeriya akayi karawar.
A karshen mako Najeriya zata je Doula inda zata sake karawa da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, yayin da Cape Verde zata kara da Liberia.
A wani labarin na daban hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF ta amince da kuskure a lissafin da ta yi a baya kan alkaluman fitowar kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa wasanni tare da tawagar kasar.
Yayin da NFF a baya ta ce Musa ya buga wa Eagles wasanni 100, FIFA ta ce sam wasanni 98 ya dokawa tawagar Super Eagles ta Najeriya ciki harda haduwar da sukayi da Cape Verde a wasan neman gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2022.
Cikin sanarwar FIFA a ranar Talata ba a kirga fitowar Musa ba a karawar su da Togo a wasan sada zumunci da aka yi a Paris a watan Yunin shekarar 2017 da kuma wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta Rasha 2018 da Algeria a Constantine a watan Nuwambar 2017. Saboda kurakurai da aka tafka da suka saba dokokin FIFA.