Zuwa yanzu ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya akalla 18 ne suka hallara a sansanin atisayen kasar da ke birnin Abuja cikin ‘yan wasa 25 da kasar ta kira don tunkarar karawarsu da Black Stars ta Ghana a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Kaftin din tawagar ta super eagles Ahmed Musa da mataimakinsa Williams Ekong na jerin ‘yan wasan farko da suka hallara a Abuja, baya ga Leon Balogun da Oluwasemilogo Ajayi da kuma Olaoluwa Aina da Frank Onyeka.
Sauran ‘yan wasan da suka hallara sun hada da Odion Ighalo da Daniel Akpeyi da kuma Oghenekaro Etebo sai Kelechi Iheanacho da Abdullahi Shehu da kuma Francis Uzoho sai Moses Simon.
Sauran sun hada da Emmanuel Dennis da Joseph Ayodele-Aribo da kuma Calvin Bassey da Innocent Bonke da Kenneth Omeruo.
Za dai a doka wasan ne ba tare da mai tsaron ragar Najeriya lamba daya ba wato Maduke Okoye wanda aka maye gurbinsa da John Noble mai tsaron ragar Enyimba.
Najeriyar wadda ta dage kofin Afrika sau 3 za ta hadu da Ghanar wadda ta dage kofin sau 4 a filin wasa na Baba Yara mai daukar ‘yan kallo dubu 40.
Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles doke Guinea Bissau a gasar cin kofin Afrika da Kamaru ke karbar bakwanci da ci 2 da nema.
A wannan fafatawa tsakanin Najeriya da Guinea Bissau bayan mituna 57 na wasan Sadiq daya daga cikin yan wasan gaban Najeriya ya huda ragar Guinee, kazalika bayan mituna 75 William Troost Ekong dan shekaru 28 mai sanye da lamba 5 ne ya zura kwallo ta biyu a ragar Guinee Bissau,duk da rashin amincewar alkalin wasa, sai da aka koma bangaren na’urar nan ta VAR, wanda hakan ta tabbatar da cewa kwallon na Ekong ya halita.
A yau alhamis 20 ga wannan wata na Janairu, Aljeriya zata ketse reni da Cote D’Ivoire a rukunni na biyar, Saliho a na ta geffen za ta kara da Guinee Equatorial.