A jiya Juma’a 2 ga watan Yunin nan ne kwamitin tsaron MDD, ya amince da kudurin tsawaita wa’adin aikin tawagar tallafin jin kai dake aiki a kasar Sudan, zuwa ranar 3 ga wayan Disambar karshen shekarar nan.
Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce manyan burikan sassan kasa da kasa su ne wanzar da zaman lafiya da daidaito a kasar Sudan.
Kuma Sin na jaddada kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a rikicin kasar, da su gaggauta dakatar da bude wuta, tare da kawo karshen yakin da suke gwabzawa.
Geng Shuang, ya kara da cewa, ya kamata sassan da batun ya shafa su warware dukkanin sabani, da bambance-bambancen dake tsakanin su ta hanyar siyasa, su kuma samar da yanayi na cimma burin dakatar da bude wuta mai dorewa, da kuma tsare-tsaren siyasa. (Saminu Alhassan).
A wani labarin na daban gwamnatin Kogi ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Gwamna Yahaya Bello hari a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Ta ce an kai harin ne a kusa da wani sansanin sojin ruwa, mai tazarar kilomita kadan daga Lokoja, babban birnin jihar.
Kwamishinan yada labaran Jihar Kogi, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja.
Fanwo ya yi zargin cewa ‘yan bindigar ‘yan barandan siyasa ne na wata jam’iyyar adawa ta SDP a jihar.
Kwamishinan ya ce lamarin da ya faru da misalin karfe 12:30 na rana, ya yi sanadin jikkatar mutane da dama da suka hada da jami’an tsaro wanda aka kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.
“’Yan bindigar da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne na jam’iyyar SDP, da suka hango ayarin Bello suna tahowa, sai suka tare hanya suka fara harbinsu.
“Amma Alhamdulillahi gwamnanmu ya tsira ba tare da samun wani rauni ba.
“Wasu mataimakan tsaro da sauran masu taimaka wa gwamnan sun samu raunuka, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da su.
“Muna kira ga jama’ar Kogi da su kwantar da hankalinsu domin jami’an tsaro suna bincike dk cafke ‘yan bindigar da suka kai harin,” in ji shi.
Fanwo ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da karya doka da oda ba amma za ta yi duk mai yiwuwa domin gurfanar da maharan a gaban kuliya.
A cewarsa, gwamnan ya yi gargadin cewa kada wani dan jam’iyyar APC ya shiga duk wani harin ramuwar gayya domin hakan na iya haifar da rashin tsaro.
Da yake mayar da martani, Mista Kunle Afolayo, mai taimaka wa dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Yakubu Ajaka, a fannin yada labarai, ya musanta zargin magoya bayan jam’iyyar ne suka kai harin.
“Shin zai yiwu jam’iyyar siyasa ta adawa ta kai wa gwamna hari haka?
“Muna kan hanyarmu ta zuwa fadar Maigari da ke Lokoja daga Koton Karfe a yammacin yau, sai ayarin motocin gwamnan da suka nufi Lokoja daga Abuja suka same mu a hanya, suka kai mana hari.
“Allah ya san gaskiya. Abin takaici ne yadda gwamnatin APC a Kogi ke amfani da karfin gwamnati a kanmu tare da yi mana kazafi kan laifin da suka aikata mana,” in ji shi.