Kamar yadda kafar sadarwa ta ABNA ta rawaito, a wajen taron jawabai wanda wanda kwamitin goyon bayan Islamic Resistance ya shirya a birnin Khartoum, shugabannin addini sun nuna damuwar su bisa mamayar masallachin Qudus mai alfarma.
Kamfanin dillacin labari na Ahlulbayt (ABNA) ya rawaito cewa, shugabannin addinin a kasar Sudan saunyi Allah wadarai da ‘yan sandan mamaya kan zagaye wannan masallachi gami da kai hari kan wadanda suke ciki.
Shugaban masu fafutukar Musulunci Muhammad Ali al-Jizoul ya bayyana cewa, taron yazo ne cikin sharin huldar shari’ar Sudan da al’ummar Palestine duba da zaluncin da yahudawan sahayoniya ke aiwatarwa a kan raunana.
Ali al-Jizoul ya bayyana cewa, a watanni hudu da suka gabata musulmai 10,000 aka raba da muhallan su.
A nasa bangare sakataren matasa na harkar musulunci Hamed Abdel Rahman ya bayyana cewa, al’amarin falasdinu shine babban lamarin al’umma kuma babu wani tsaka tsaka a cikin sa, ya kuma jadadda cewa dole ne akwato Palestine gabadaya.
Kafara sadarwa ta Ahlulbayt (ABNA) ta kuma rawaitowa cewa k a kasar morocco ma an gabatar da zanga zangar nuna goyon baya ga Palestine da Al-Aqsa.
A kwanakin da suka gabata dai an samu hatsaniya sakamakion kutsen da ‘yan sandan mamaya sukayi a masallachi mai alfarma na Qudus tare da kawar da mas ibada da karfi daga cikin sa.
Mutane daga sassa daban daban na duniya suna cigaba da nuna damuwar su dangane da halin da Falasdinawa suke ciki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, duk da kaka gida da sojojin mamaya sukayi amma musulmi sun gudanar da sallar juma’a a masallachin tattare da rera wakokin neman ‘yanci.