Rikicin da ya barke a yankin Darfur na kasar Sudan tsakanin kungiyoyin Larabawa dasauran kabilu ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 100, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Hashem ya ce an kashe mutanen ne mafi yawa a tsakanin kabilar Gimir a lokacin arangamar, amma ba a bayyana adadin mutanen da aka kashe a cikin kabilar Larabawa ba.
Fadan dai ya barke ne a makon da ya gabata bayan wata takaddamar gonaki tsakanin mutane biyu da suka fito daga kabilun biyu..
A cikin watan Afrilu, sama da mutane 200 ne aka kashe a fadan da aka gwabza tsakanin kabilun Larabawa da na Gimir a yammacin Darfur.
Yankin Darfur na sudan dai ya kasance cikin yakin basasa a tsawon shekaru uku a lokacin mulkin shugaba Omar al-Bashir.
Yayin da wasu manyan kungiyoyin ‘yan tawayen sudan suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 2020, har yanzu munanan tashe-tashen hankula na ci gaba da kamari kan rikicin filaye da dabbobi.
A wani labarinn na daban ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikata biyar na kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF a Arewa mai Nisa da ke kasar Kamaru, yankin da ke fama da matsalar ‘yan tada kayar baya.
Kungiyar likitocin da kuma wani babban jami’in yankin na Arewa mai Nisa a Kamarun sun lamarin ya auku ne a Alhamis da ta gabata, inda wasu mutane dauke da makamai a Fotokol, kusa da kan iyaka da Najeriya, a suka shiga wani gini da MSF ke amfani da shi, suka kuma sace jami’ai 5.
Mutanen da aka yi garkuwa da su, sun hada da ma’aikatan agaji uku da suka fito daga kasashen Chadi, Senegal da Ivory Coast, da kuma jami’an tsaron Kamaru biyu.
Yankin Arewa mai nisa a Kamaru da ke fama da matsalolin tsaro ya yi iyaka da Najeriya daga bangaren yammacinsa, yayin da kuma daga bangaren gabashi yayi iyaka da kasar Chadi, wadanda su ma suke fafutukar murkushe hare-haren ‘yan ta’adda.