Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan matsayin na gab da zama kasa mafi fama da yunwa sanadin yaki a duniya, bayanin da ke zuwa bayan watanni 11 da fara yakin kasar.
Rikicin da ke tsakanin Jagoran gwamnatin sojin kasar, Abdulfattah AlBurhan da shugaban rundunar kai daukin gaggawa ta RSF, Mohammed Hamdan Daglo, ya lakume rayukan dubban mutane tare da rusa kasar da kuma durkusar da tattalin arzikinta.
Yakin na watanni 11 ya raba mutane sama da miliyan takwas da muhallansu, abin da ya sanya yakin matsayin wanda ya fi kowanne haddasa hijira a duniya.
Da ta ke jawabi, shugabar hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya, Cindy McCain, ta ce a yanzu yunwa ita ce babbar barazanar da fararen hula a Sudan ke fama da ita.
Shekaru 20 da suka gabata yankin Darfur shi ne mafi fama da tsananin yunwa sanadin yaki a duniya, sai dai yanzu akwai yiwuwar yankin ya yi kunnen-doki da Sudan.
McCain, ta nuna takaicinta kan yadda duniya ta manta da Sudan da irin tsanannin da fararen hular kasar ke ciki duk a sakamakon yakin da za a iya magance shi ta hanyar masalaha.
Ministan Lantarki, Bayo Adelabu, ya yi barazanar kwace lasisin kamfanonin rarraba wuta na Discos, yana mai cewa ba za a lamunci yanayin da suke saka mutane na karancin wutar ba.
A wani labarin na daban ministan, wanda ya wallafa sakon barazanar a shafinsa na X a ranar Laraba.
Ya ce ya damu matuka da tabarbarewar samar da wuta da ake fama da rashin ta a fadin kasar nan.
“Don haka ne ma na kira shugabannin Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC) da na Ibadan (IBEDC), da kuma shugaban Kamfanin Samar da Lantarki na Nijeriya TCN don yin wata ganawa mai muhimmanci,” in ji ministan.
Ya ce ya kira taron ne don tattaunawa kan yadda ake matukar fama da matsalar samun wuta a wadannan yankunan da kuma nemo mafita.
Yanzu haka dai ana matukar fama da karancin wuta a wasu sassan Nijeriya, musamman babban birnin tarayya, Abuja a daidai lokacin da yanayin zafi ke kara kunno kai.
“Abin takaici ne ganin yadda ake samun raguwar wutar lantarki duk da kokarin da ake yi na inganta lamarin.
“Ma’aikatar Lantarki ta matsa lamba kan Kamfanonin da ke Samar da Wutar (GENCOs) don inganta ayyukansu, lamarin da ya sa aka samu karuwar samar da wuta zuwa sama da megawat 4000,” a cewar Ministan.
Sai dai Mista Adelabu ya bayyana cewa duk da wannan ci gaba da ake samu, wasu kamfanonin sun gaza rarraba wutar da TCN ke bayarwa yadda ya kamata.
Ya kuma koka kan yadda yawan barnar kayayyakin samar da wutar da ake yi ke kara ta’azzara matsalar a Abuja da Benin da Fatakwal da kuma Ibadan.
DUBA NAN: Za’a Daina Hada Hadar Binance A Najeriya
Minista Adelabu ya sha alwashin cewa daga yanzu zai kama dukkan kamfanonin rarraba wutar da alhaki idan har ba su yi abin da ya dace ba.