Ofishin jakadancin kasar Masar a birnin Khartum na kasar Sudan ya musanta labarin cewa shugaban kasar ta Masar Abdul Fattah Assisi ya ziyarsi birnin Khartum babban birnin kasar Sudan inda ya gana da shugaban sojojin kasar Abdufattah Alburhan a asirce.
Jaridar Sudan Tribune ta nakalto jakadan kasar Masar a birnin Khartum Hossam Issa yana fadar haka ya kuma kara da cewa wasu kafafen yada labarai wadanda ba’a sansu bane suka yada wannan kariyar. Issa ya kammala da cewa idan shugaban kasar Masar zai zo Khartum za’a bada sanarwan zuwansa ba aboye ba.
A makon da ya gabata ne wasu kafafen yada labarai suka yada labarin cewa Assisi tare da ministan ayyukan leken asirinsa da wasu ministoci sun kawo ziyara na kwana guda a birnin Khartum inda suka gana da Shugaba Burhan.
Shugaban kasar Masar ne kadai yake goyon bayan Burhan a fafatawar da yake yi da masu zanga zanga wadanda suke adawa da juyin mulkin ranar 25 ga watan Octoban shekarar da ta gabata.