Sudan; Lauyoyi Masu Kare Al-Bashir Sun Yi Watsi Da Batun Gurfanar Da Shi A Gaban Kotun ICC.
Tawagar lauyoyi da ke kare hambararren shugaban Sudan Omar al-Bashir, ta ki bayyana gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, tare da jaddada cewa ba ta da hurumin yi wa wani dan Sudan tambayoyi.
Wani mamba a kwamitin Hashem Abu Bakr al-Jaali ya bayyana a wata hira da manema labarai cewa, hukumar shari’a ta Sudan na da hurumin da za ta iya yi wa wanda yake karewa shari’a, bisa la’akari da cewa bangaren shari’ar na Sudan a halin yanzu, ya hada da hukumcin laifuffuka masu alaka da laifukan yaki da cin zarafin bil’adama, sabanin yadda ake gudanar da shari’ar a baya, wanda hakan ke bayar da damar gurfanar da duk wanda ake tuhuma bisa irin wadannan zarge-zarge.
READ MORE : Iran; Amurka Da Turai Ba Su Da Wani Zabi Da Ya Wuce Su Amince Da Yarjejeniyar Nukiliya.
Ya ci gaba da cewa, a da, dokar kasar Sudan ba ta kunshe da hukumcin laifuka da ake kira laifuka na dokokin jin kai na kasa da kasa, wadanda laifukan yaki ne da ke kunshe a cikin yarjejeniyar Geneva ta shekarar 1949, wadda Sudan ta amince da su, amma ba a shigar da dokar cikin kundin dokokin hukunta laifuka na kasar Sudan ba.