Sudan; Ana Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Neman Kafa Gwamnatin Farar Hula Zalla.
A babban birnin kasar Sudan Khartoum, da wasu yankuna na kasar an gudanar da zanga-zangar tunawa da zagayowar ranar hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir, kamar yadda kuma masu gangamin suka bukaci sake dawo da mulkin farar hula zalla a kasar.
An kaddamar da gagarumin gangamin na miliyoyin mutane ne domin tunawa da ranar 11 ga watan Afirilu wato lokacin hambarar da gwamnatin Albashir, kamar yadda kuma suka nuna rashin amincewarsu da ci gaba da yin babakere da sojoji ke yi a kan mulkin kasar.
Ganin yadda jama’a ke ta matsin lamba a kan hukumar soji, kwamitocin adawa sun fara tsara sahunsu, tare da yin watsi da duk wasu bambance-bambancen da ke tsakaninsu, tare da hada kansu domin tunkarar mataki na gaba.
READ MORE : Nasrullah; Abin Da Ke Faruwa A Falastinu Manuniya Ce Kan Makomar Isra’ila.
Sojojin kasar Sudan dai sun kwace mulki ne bayan da al’ummar kasar suka nuna rashin gamsuwa da mulkin Alabshir, tun daga lokacin kuma suke ci gaba da mamaye madafun iko na kasar.
READ MORE : Iran da Qatar Sun Rattaba Hannu Kan Wasu Yarjeniyoyi Na Hadin Gwiwa Guda 6.
READ MORE : ‘Yan bindiga sun kashe mutum fiye da 130 a Jihar Filato.