Sudan; Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Sojoji A Kasar.
Duban mutanen kasar Sudan suna ci gaba da fitowa kan titunan biranen kasar inda suka dage kan cewa dole ne gwamnatin sojojin kasar ta mika mulki ga fararen hula, wadanda zasu gudanar da zabubbuka su kuma fitar da kasar daga matsalolin tattalin arzikin da take fama da su.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Litinin ma dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Khartum babban birnin kasar da kuma wasu biranen don neman sojojin su mika mulki ga fararen hula ba tare da bata lokaci ba.
READ MORE : Burtaniya; Wata Babbar Kotu Ta Amince Da Maida Yan Gudun Hijira Rwanda.
Kafin haka dai bayan juyin mulkin da aka yiwa Bashir shekaru biyu da suka gabata, sojojin sun sake yin juyin mulki a cikin watan Octoban da ya gabata wanda ya kawo karshen gwamnatin hadakan na rikon kwarya da suka kafa.
READ MORE : Lebanon Ta nisanta yiwuwar bullar yaki tsakaninta Da Isra’ila kan Rikicin kan iyaka.
READ MORE : Burkina Faso – ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Akalla Mutane 50.
READ MORE : Kotun Senegal Ta Zartas Da Hukuncin Dauri Akan Shugaban ‘Yan Tawayen Casamance.