Sudan; An Saki Wasu ‘Yan Zanga-Zangar Da Aka Kama A Kasar Sudan A Jiya Litinin.
Gwamnatin sojoji a kasar Sudan sun sallami wasu masu zanga-zanga wadanda suke tsare da su a lokacin zanga-zangar kin jininsu bayan juyin mulkin da suka yi a cikin watan Octoban da ya gabata.
Sakin fursinonin na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin suka dage doka ta baci wacce suka kafa bayan juyin mulkin da suka yi a cikin watan Octoban shekarar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa sojojin sun sallami mutane 24 a birnin Port Sudan, sannan wasu 39 a wani wuri kusa da birnin Khartum babban birnin kasar.
Labarin ya kara da cewa har yanzun akwai mutane kimani 50 a tsare saboda sojojin na zarginsu da kashe jami’an tsaron kasar a lokutan zanga-zangarsu. Banda haka sojojin sun sake wadanda suka tsaren ne don bude kofar tattaunawa da shuwagabannin yan adawa da gwamnatinsu.
READ MORE : Majalisar Dokokin Yemen Ta gabatar Bukatar Kafa Doka Ta Haramta Hulda Da Isra’ila.
Haka kuma sakin ya zo dai dai da ziyarar da wani jami’an MDD zai kawo kasar a kokarin sasantawa tsakanin sojojin da kuma ‘yan siyasa masu adawa da sojojin.
READ MORE : Zaben 2023; Dattawan Arewa Suna Son A Zabi Atiku A Shekara Mai Zuwa.