“Dole ne mu yi duk mai yiwuwa don ganin Isra’ila ta yi biyayya ga hukuncin Kotun Duniya (ICJ),” in ji Ministan Harkokin Wajen Spain.
“Abin da muka gani a cikin ‘yan kwanakin nan shi ne matakan taka tsantsan… na wajibi ga kowane bangare… ba a bin su… kasancewar ba sa bambance hare-haren soji da na farar hula, cewa suna kai hari asibitoci da makarantu… ba son yin biyayya ba ne,” in ji Jose Manuel Albares a wata hira da jaridar El Pais ta Spain ta buga.
Matakin dai ba wai don “a yi adawa da Isra’ila ba ne” amma don “dakatar da yakin,” kamar yadda ya fada wa El Pais, ya kara da cewa Spain ta riga ta fara aiki kan wani rahoto, wanda zai iya wuce shafuka 100, kan lamarin.
“A cikin wannan takarda, muna goyon bayan ayyukan kotun, ba tare da yin riya cewa mu muka maye gurbinta ba,” in ji Ministan.
Da aka tambaye shi ko ya kamata a sanya wa Isra’ila takunkumi idan ba ta bi su ba, Albares bai amsa kai tsaye ba, a maimakon haka ya ce dole ne kasashe su yi duk mai yiwuwa don tilasta wa gwamnatin Isra’ila yin hakan.
DUBA NAN: Khan: Wata Kotu A Pakistan Ta Saki Imran Khan
A wani labarin na daban Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu ta Majakisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi gargaɗin cewa za a samu ɓarkewar annobar amai da gudawa a Gaza a yayin da ake fama da matsanancin ƙarancin ruwa sakamakon hare-haren Isra’ila.
A sanarwar da ta fitar, UNRWA ta ƙara da cewa “A yayin da ake ci gaba da fama da tsananin rashin tsabtataccen ruwan sha da kuma tsananin zafi a Zirin Gaza, akwai barazanar ɓarkewar cututtuka da motsewar jiki saboda rashin ruwan sha.”
“Akwai damuwa sosai cewa kwalara na iya ɓarkewam lamarin da ka ita ta’azzara mummunan yanayin da mutane ke fama da shi.”