Somalia; Shugaban Kasar Ya Shelanta Yaki Da Kungiyar Al-Shabab Ta Yan Ta’adda.
Shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mahmood ya shelanta yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-Shabab ta kasar bayan taron da ya gudanar da majalisar tsaron kasar a fadarsa a birnin Magadishu babban birnin kasar a jiya Talata.
Majiyar muryar JMI ta nakalto shugaban yana cewa a halin yanzu gwamnatin kasar zata aiwatar da shiri na musamman don kwace iko a wasu yankunan da kungiyar ta Al-Shabab take iko da su a cikin kasar.
Shugaban yayi wannan maganar ne kwanaki kadan bayan da kungiyar ta kai hare-hare kan Otel mai suna ‘Hayat’ a cikin birnin Magadishi a ranar jumma’an da ta gabata, hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 13.
An kafa kungiyar Al-shabab wacce take da ra’ayin kungiyar al-ka’ida ne tun shekara ta 2004, kuma a wani lokaci sai da ta gaiga karbi iko da birnin Magadishu babban birnin kasar.
READ MORE : Iran; Shugaban Hukumar IAEA Shi Ne Babbar Mai Kafar Ungulu A Farfado Da JCPOA.
Kuma a halin yanzu kungiyar tana iko da wasu yankuna a kasar ta Somalia. A wasu lokutan kungiyar takan kai hare-hare hare kan kasahe makobta da kasar Somalia wadanda suka hana da Kenya da kuma Habasha.