Sojojin Sudan sun janye daga yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta in ji wasu kafofi
Jami’an gwamnatin Sudan sun ce sojojin kasar sun dakatar da tattaunawar dakatar da bude wuta da dakarun kar-ta-kwana na RSF, inda suke zargin ƴan kungiyar da saba yarjejeniyar akai-akai.
Sojojin sun ce sun dauki matakin ne saboda dakarun kungiyar wadanda suka kira ƴan tawaye sun ki bin sharudan yarjeniyoyin da aka yi na baya ko da guda daya, wadanda suka hada da janyewa daga asibitoci da unguwannin da jama’a ke zaune, kamar yadda wani jami’in gwamnati da ya nemi kada a bayyana sunansa ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Haka kuma wani jami’in diflomasiyya na Sudan ma ya fada wa Reuters, batun janyewar sojojin na Sudan daga tattaunawar yarjejeniyar wadda ake kokarin tabbatarwa domin bayar da damar kai kayan agaji ga wadanda suke matukar bukata.
Dukkanin bangarorin biyu na Sojin da na RSF babu wanda ya fito fili ya yi magana a kan janyewar.
A ranar Litinin masu shiga tsakani daga Saudiyya da Amurka suka ce sojojin da RSF sun amince su tsawaita yarjejeniyar da kwana biyar.
Sai dai kuma an ci gaba da fada a sassa daban-daban na kasar ciki har da babban birnin kasar Khartoum, inda RSf ta ce an kai wa inda dakarunta suke hari.
Su ma sojoji sun ce sun kawar da wani hari da RSF ta kai a birnin El-Obeid na tsakiyar kasar.