Sojojin Rasha Sun Shiga Birni Na Biyu Mafi Girma Na Ukraine.
A yayin da aka shiga kwana na hudu na matakin sojin da kasar Rasha ta dauka kan Ukraine, rahotanni na cewa sojojin Rashar sun shiga Kharkiv birni na biyu mafi girma na Ukraine a arewa maso gabas.
Mahukuntan binrin sun bukaci jama’ar yankin kimanin miliyan 1,4 da kowa ya zamna gida.
Kafin nan rundinar sojin Rasha, ta ce ta yi manyan biranen kudancin Ukraine biyu kawanya.
Bayanai sun ce a cikin sa’o’I 24 da suka gabata sojojin na Rasha sun gewaye biranen na Kherson et Berdiansk.
A wani jawabi da ya yi wa al’ummar kasar Rasha ta talabijin, shugaba Vladimir Putin ya yaba tare da godiya ga sojojin Rasha da ya yi ikirarin cewa suna gudanar da ayyukansu a Ukraine yadda ya kamata.
A ranar Asabar dai kasashen turai, sun sanar da kara tsauraren takunkumansu kan Rasha, game da matakin data dauka kan Ukraine din, ciki har da dakatar da wasu bankunanta daga tsarin nan na bayar da bayanai kan harkokin kudade a bankuna da ake ma Swift.