‘Sojojin Najeriya sun yi ruwan wuta kan ƴan bindiga a dazukan Kaduna’
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce dakarun Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama da ƙwato makamai masu ɗinbin yawa a wani samame da suka kai a wasu dazukan jihar.
Gwamnatin ta ce an samu nasarar hakan ne sakamakon hare-haren da sojojin suka kai ta sama.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewar an kai hare-haren ne a ƙananan hukumomin Igabi, da Giwa, da Chikun da Kajuru.
Kwamishinan ya ƙara da cewa a lokacin waɗannan hare-hare an samu nasarar kashe ƴan bindiga da dama, da kuma tayar da daba-daba na masu garkuwa da mutane.
Sai dai kwamishinan ya ce har yanzu babu takamaiman alƙaluma na waɗanda aka kashe ko kuma makaman da aka ƙwato daga ƴan fashin.
Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaron sun samu nasarar ceto mutane da dama da ake garkuwa da su.