Sojojin Najeriya Sun Sake Kama Babban Dan Kungiyar ISWAP Wanda Ya Tsere Daga Kurkukun Kuje.
Ma’aikatan tsaro a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan sake kama wani jigo a cikin kungiyar yan ta’adda ta ISWAP mai suna Idris Ojo wanda yake daga cikin fursinonin da suka tsere a harin gidan yarin Kuje a Abuja a cikin watan da ya gabata.
Shafin yanar gizo na Sahara Reporters ya nakalto shugaban hafsoshin tsaro na tarayyar Najeriya yana Lucky Irabor yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa an sake kama Idris Ojo ne a jihar Ondo.
A ranar 5 ga watan Yulin da ya gabata ne wasu yan bindiga wadanda ake zaton mayakan book haram ne suka kai hari kan gidan yarin Kuje a Abuja babban birnin kasar inda suka sake fursinoni fiye da 500. Daga cikinsu akwai yayan kungiyar ta Boko Haram da dama.
Irabor ya kara da cewa sojojin kasar tare da tainakon yansandan farar hula ta DSS sun sami nasarar kama wadanda suka kai hari a cocin Owo .
Jami’in sojojin Najerian ya kara da cewa an kama tare da Idris Ojo Jimo Ibrahim, dana shekara 39 a duniya da Idris Abdulmalik Omeiza, ko wanda ake kira Ibn Malik, da Momoh Abubakar, Aliyu Itopa da kuma Auwal Onimisi. Duk sun aikata laifuffuka daban-daban suka tsare. A halin yanzu suna shiga hannun jami’an tsaron kasar.