Hare-haren da Isra’ila ta kwashe kwana 55 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara.
Kimanin mutum 7,000 aka danne a baraguzan gine-gine wadanda Isra’ila ta yi wa luguden wuta, a cewar hukumomi.
Kungiyar ta Falasɗinu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan Falasɗinawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365.
1024 GMT — Isra’ila ta ce sojojinta sun daƙile wani hari daga Labanon
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta dakile wani hari ta sama da ya tsallaka daga Lebanon, a wani lamari da ya dagula yanayi zaman lafiyar da ake samu a kan iyakar tun bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da Isra’ila suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi.
Shaidu na Reuters sun ji ƙarar tashin bama-bamai a yankin kudu maso gabashin Lebanon. Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗauki alhakin duk wani hari daga kasar Labanon ɗin.
Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta Lebanon sun shafe makonni suna musayar wuta a kan iyakar kasar. Sauran kungiyoyi da suka hada da Hamas da kungiyar Jihad Islama ta Falasdinu su ma sun kaddamar da hare-hare daga Lebanon kan Isra’ila a lokacin rikicin.
1130 GMT — Sojojin Isra’ila sun sake kama Falasdinawa 40 a Yammacin Kogin Jordan
Rundunar sojin Isra’ila ta tsare aƙalla Falasɗinawa 40 a wani samame da ta kai Yammacin Kogin Jordan da safiyar ranar Alhamis, a cewar Ƙungiyar Fursunoni ta Falasɗinawa.
Kungiyar ta Falasɗinu mai zaman kanta ta bayyana cewa kamen na baya-bayan nan ya sa yawan Falasɗinawan da aka tsare tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 3,365.
Tashin hankali na ƙaruwa a Yammacin Kogin Jordan a yayin da sojojin Isra’ila ke kai hare-hare Zirin Gaza tun bayan harin ba-zatan da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.
1200 GMT — An kashe mutum uku a harin da aka kai a Gabashin Birnin Ƙudus
Aƙalla mutum uku ne suka mutu sannan shida suka jikkata, ciki har da biyun da ke cikin wani mummunan yanayi, a wani harbe-harbe da aka yi a yankin Gabashin Birnin Kudus da Yahudawa ƴan kama wuri zauna suka mamaye.
‘Yan sanda sun ce a ranar Alhamis din nan an kashe mutum biyu da ake zargi da hannu a harbe-harben a nan take bayan harin da aka kai a kusa da tashar motar bas da ke Yammacin Birnin Kudus, inda babu shingayen binciken ababen hawa da ke gadin hanyar shiga birnin.
‘Yan ta’adda biyu ne suka isa a mota, daya daga cikinsu dauke da M-16, ɗaya kuma ɗauke da bindiga,” inda suka buɗe wuta, kamar yadda shugaban ‘yan sandan Kudus, Doron Torgeman ya shaida wa manema labarai a wurin.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Magen David Adom ta ce daya daga cikin waɗanda abin ya shafa wata mace ce mai shekara 24 da haihuwa.
Harin na zuwa ne jim kadan bayan da aka tsawaita wa’adin tsagaita wuta a Zirin Gaza tsakanin mayaƙan Falasdinawa da Isra’ila na tsawon kwanaki bakwai, kafin cikar wa’adin.
0455 GMT — Isra’ila da Hamas sun amince a kara wa’adin tsagaita wuta da kwana daya
Isra’ila da kungiyar Hamas mai rajin kare hakkin Falasdinawa sun amince su tsawaita yarjejeiyar tsagaita zuwa karin kwana daya.
Kazalika sojojin Isra’ila sun ce za a ci gaba da mutunta yarjejeniyar “bisa kokarin masu shiga tsakani na ci gaba da ganin an saki karin mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma a kan sharudan da aka yarda da su.”
Kasar Qatar wadda ke shiga tsakani ta tabbatar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince su tsawaita wa’adin yarjejeniyar.
0200 GMT — An gaya wa mayakan Hamas su sanya damara don ci gaba da yaki
Kasashen duniya na matsa lamba kan Isra’ila da Hamas domin su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta bayan sun yi musayar karin fursunoni sannan an bar karin kayan agaji sun shiga yankin Gaza da aka mamaye.
Sai dai “Majalisar Yaki” ta Isra’ila ta kammala taronta ba tare da cim ma matsaya kan tsawaita yarjejeniyar ba, kamar yadda TRT World ta fahimta. Wasu kafofin watsa labarai na Isra’ila sun ambato majiyoyi suna cewa “jerin sunayen karin mutanen da Hamas ta nemi a sako bai cka sharudan” Isra’ila ba.”
Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta daina aiki ne da misalin karfe 7 na safe a agogon Gaza, wato karfe 5 a agogon GMT.
Sashen soji na kungiyar Hamas ya shaida wa mayakansa su daura damarar komawa yaki da Isra’ila idan ba a tsawaita yarjejeniyar ba.
“Al-Qassam Brigades yana umartar dakarunsa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a awannin karshe na karewar yarjejeniyar,” in ji sanarwar ya fitar. An bukaci mayaka su shiga cikin “damara har sai an fitar da sanarwa a hukumance game da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.
Source: TRThausa