Sojojin Isra’ila Sun Kashe Wani ba falesdine Da Kuma Harbe Wasu Matasa A Birnin Quds.
Rahotanni daga yankin Falesdinu sun nuna cewa sojojin Isra’ila sun yi harbi kan mai uwa da wabi da hakan ya yi sanadiyar wani ba falesdine da kuma harbe wasu matasa guda biyu a daidai lokacin da rikcin yake kara kamari sakamakon shirin da isra’ila ke yi na korar falesdinawa daga tsohon garin binirn Quds.
Rahotan da kamfanin dillancin labaran falesdinu Wafa ya fitar ya nuna cewa da safiyar yau ce sojojin Isra’ila sun afkawa sansanin yan gudun hjira na Balata dake garin Nablus a arewa da gabar yammacin kogin jodan, domin kama wasu falesdinawa da hakan ya jawo rikici tsakaninsu da mazauna yankin. Inda suka yi amfani da harsashi mai rai wajen tarwatsa su.
Minsitan lafya na yankin falasdinu ya fadi cewa wani matashi bafalasdine dan shekaru 17 da haihuwa mai suna Nader Haytham rayan anga harsashi mai yawa a kansa da kirjinsa da kuma hannunsa wanda anan take yayi shahada.
READ MORE : Rasha Ta Kakabawa Manyan Jami’an Amurka Takunkumi.
Fira ministan Falesdinu Mohammad Shteyye ya zargi isra’ila da fakewa da shagaltuwa da manyan kasashen duniya suka yi da rikicin Ukrain wajen fadada kai hararenta a yankunan falesdinawa.