Sojojin Isra’ila Sun Kashe Falasdinawa Biyu.
Ma’aikatar kiwon lafiyar Falasdinu ta sanar da mutuwar wani matashin bafalasdine na biyu a wannan rana sakamakon harbin bindiga na sojin Isra’ila yammacin kogin jodan da ta mamaye.
Alaa Shaham, mai shekara kimanin ashirin ya mutu ne sakamakon harbin bindiga a kai na sojojin Isra’ila a yankin Qalandia dake tsakanin birnin Qudus da Ramallah.
READ MORE : Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Takwaransa Na Ukraine.
Shi kuwa Nader Haitham Rayan, mai shekara 16, ya mutu ne sakamakon harbinsa da da sojojin na Isra’ila sulayi masa da harsashai masu yawa a kirji da kuma kai, a sansanin ‘yan gudun hijira na Balata kusa da Naplouse, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiyar ta falasdinu ta sanar, saidai ba tare da yin bayyani ba kan sanadin faruwar lamarin.
Sau tarin yawa dai akan samu arangama tsakanin falasdinuwa Da kuma jami’an tsaron Isra’ila dake kai samame a yankunan Falasdinun da suka mamaye tun cikin 1967.
READ MORE : An Shiga Kwana Na Ashirin Na Rikicin Rasha Da Ukraine.