A kalla falasdinawa dari ne suka ji rauni yayin da sojojin haramtacciyar kasar isra’ila suka kai harin kana mai uwa da wani bisa kan masu muzaharar murnar kubutar wasu falasdinawa guda shidda da gwamnatin haramtacciyar kasar isra’ilan ke tsare dasu ba bisa ka’ida ba.
Su dai falasdiawan wadanda aka tsare su a kurkukun Gilboa jail dake banagaren haramtacciyar kasar isra’ilan sun samu nasarar kubuta ne yayin da suka haka rami kuma suka bi ta ciki suka tsare daga kurkukun.
Kamar yadda gidan jarida na Aljazeera ya rawaito bayan samun labarin kubutar falasdinawan ne sai al’ummar falasdinu suka fito tituna suna muzahara domin nuna farin cikin su da wannan babbar nasara da ‘yan uwan su suka samu na kubuta da kurkukun zalunci na yahudawan haramtacciyar kasar isra’ila, wanda a yayin muzaharar ne sojojin na haramtacciyar kasar ta isra’ila suka kawo harin kuma a take suka raunata a kalla mutane dari.
Sojojin na haramtacciyar kasar isra’ila sun dingi harba barkonon tsohuwa, harsasan roba da sauran makamai a yankin ”west bank” wanda a take yayi sanadiyyar raunatar a kalla mutane dari daga cikin masu muzaharar lumana din.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an dai gudanar da muzaharorin na lumana a yankunan Ramallah, Nablus, Bethlehem, da kuma Hebron, sa’annan kuma da wasu kauyuka dake kusa da zirin gaza wadanda suma suna cikin matsin lamba gami da zaluncin sojojin na haramtacciyar kasar ta Isra’ila.
Rahotanni sun dai tabbatar da cewa kullum rana sojojin haramtacciya kasar isra’ila suka kaddamar da sabon salon zalunci a kan raunana falasdinawa a yayin da manyan kasashen musulmi kuma larabawa suka kama bakunan su sukayi shiru ba tare da sanya baki domin nemawa raunanan falasdinawan sassauci ko sauki daga wannan mummunan zalunci da aka dauki shekaru fiye da saba’in ana aiwatarwa a kan musulmin falasdinu.
Zuwa yanzu dai ana jiran a ji matakin da kungiyar neman ‘yancin falasdinu dinnan ta hamas zata dauka danagene da lamarin.