Sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi Bafalasdine a sansanin Aqabat Jabr da ke Jericho.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da mutuwar wani matashin Bafalasdine sakamakon harbin da sojojin Isra’ila suka yi masa a safiyar yau Talata.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa, Ahmed Ibrahim Oweidat, mai shekaru 20, ya rasu ne sakamakon munanan raunuka da ya samu biyo bayan bude wutar bindiga da sojojin Isra’ila suka yi a kansa a safiyar yau a sansanin Aqabat Jaber.”
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu, “Safa,” ya bayyana a baya cewa “maza uku sun samu raunuka sakamakon harbin da aka yi musu a lokacin arangama da sojojin mamaya na Isra’ila a sansanin Aqabat Jaber da ke kudancin Jericho.”
READ MORE : Ranar Quds a birnin London.
Rahoton ya kara da cewa, wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, wata runduna ta musamman ta Isra’ila, a boye, ta kutsa cikin sansanin lamarin da ya kai ga barkewar arangama, inda sojojin mamaya suka harba harsasai masu rai.
READ MORE : Iran; Batun Falastinu Shi Ne Mafi Muhimmanci Ga Duniyar Musulmi.
READ MORE : Rikici a Saudiyya da Kuwait game da dokar hana Doctor Strange 2.