Sojojin Isra’ila, Sun Bindige ‘Yar Jaridar Aljazeera A Yammacin Kogin Jordan.
Wata ‘yar jarida mai suna Shireen Abu Akleh, daya daga cikin shahararun ‘yan jarida na tashar talabijin ta Qatar Aljazeera, ta rasa ranta a safiyar yau Laraba sakamakon harbin bindiga da sojojin Isra’ila suka yi a yankin Jenin dake yammacin gabar kogin Jordan.
An harbe ta ne a fuska lokacin da take kan aikin daukar rahoto yayin rikici a yankin Jenine.
Baya ga ita da akwai wasu ‘yan jarida da suka jikkata a cewar rahotanni.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu da tashar Aljazeera duk sun tabbatar da mutuwar wannan ‘yar jaridar.
READ MORE : Sojojin Isra’ila sun harbe shugaban jaridar Al Jazeera.
Kisan ‘yar jaridar ta tashar Aljazeera, na zuwa ne kusan shekara guda da sojojin Isra’ila suka wargaza ginin Jalaa, wanda ya kunshi ofishin tashar ta Qatar a Zirin Gaza, a yayin rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.
READ MORE : Klopp – Ban Fidda Ran Liverpool Za Ta Iya Lashe Kofin Firimiya A Bana Ba.
READ MORE : FIFA Ta Amince Da Sake Doka Wasan Argentina Da Brazil Wanda Aka Dakatar A Bara.
READ MORE : Burkina Faso – ‘Yan Bindiga Sun Tseratar Da Fursinoni 60 A Farmakin Gidan Yarin