Sojojin Isra’ila Sun Auka Kan Masallata A Cikin Masallacin Quds Da Asubahin Yau.
Dakarun mamaya na Isra’ila sun kutsa kai cikin masallacin Al-Aqsa tare da korar masu ibada daga cikinsa, bayan da suka far musu dahayaki mai sa hawaye da harsasai masu rai.
A yau Juma’a sojojin mamaya na Isra’ila sun mamaye masallacin Al-Aqsa gaba daya, bayan fitar da dukkanin masallata daga cikinsa.
A cewar wakilin Al-Mayadeen, “Dakarun mamaya sun harba wasu abubuwa masu tarwatsewa masu tsananin kara a cikin masallacin a lokacin da ake sallar asubah, tare jefa hayaki mai sanya hawaye a kan masu ibadar, inda suka jikkata da dama daga cikinsu.”
Ya kara da cewa, dakarun mamaya sun bi sahun masu ibada, inda suka lakada musu duka, suka kuma fatattaki mafi yawansu daga cikin harabar Al-Aqsa, tare da rufe dukkan kofofin masallacin , ban da kofar Bab Hatta.
A cewar kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu, fiye da mutane 152 ne suka jikkata, wasu daga cikinsu raunukansu masu tsanani ne, sakamakon harin da dakarun mamaya suka kai kansu a cikin masallacin na Al-Aqsa.
Wanann na zuwa nea daidai lokacin da kasashen duniya suke ci gaba da yin da bakunansu a kan wannan ta’asa da Isra’ila ke tafkawa kan al’ummar Falastinu musammana cikin wannan wata mai alfarma.