Sojojin Isra’ila Na Ci Gaba Da Tsananta Kai Hari kan Masu Ibada A Masallacin Quds.
Rahotanni sun bayyana cewa han yanzu sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare hare a masallacin Quds inda suke kutsa kai har cikin masallacin sun harba hayaki mai sa hawaye da nufin tarwasta masu ibada da kokar masu yin Ittikafi a ciki, da hakan ya yi sanadiyar jikkata masu ibada da dama a masallacin.
Ana ta bangen kungiyar Hamsa ta yi barazanar mayar da martani mai zafi game da ci gaba da keta hurumin maslalacin mai tsarki da sojojin Isra’ila suke ci gaba da yi, har ila yau tab akin kakakinta ta fadi cwa taruwar da falasdinawa suka a birnin Quds da masallacin Quds ya nuna irin imani da suke das hi da gwagwarmaya a matsayin hanya daya tilo ta kwato yanci
Hizam Qasem kakakin kungiyar ta Hamas y ace irin imani da gwagarmaya da mutane Quds da sauran falasdinawa suke das hi yana kara wa kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmaya karfin guiwa na ci gaba da jajircewa wajen ganin sun yanto dukkan yankunan su da Isra’ila ta mamaye
A yan kwanakin ne a fuskanci mummuna rikici tsakanin sojojin Isra’a da falasdinawa masu Ibada tun a ranar juma 15 ga watan Aprilu inda ya zuwa yanzu akalla falasdinawa 160 ne suka jikkata yayin da sama da 400 kuma aka kama a lokacin rikicin.