Sojojin HKI Sun Harbe Wata Bafalasdinya Gabar Yammacin Kogin Jodan A Da Safe.
Rahoton da muka samu yanzu yanzu nan ya nuna cewa sojojin HKI sun harbe wata bafalasdiniya a kudu da gabar yammacin kogin Jodan bayan da suka zarge ta da yunkurin dabawa wani sojan Isra’ila wuka, adai dai lokacin da ake ci gaba da samun rikici a yankunan da Isra’ila ta mamaye a yan makwannin nan
Lamarin ya faru ne a kusa da sansanin yan gudun hijira na Arroub dake da nisa kilo mita 15 da kudancin baithlaham da safiyar yau laraba. Inda sojojin suka bude mata wuta da hakan yayi sanadiyar shahadarta.
Ministan lafiya na falasdinu ya fadi cewa a matar mai suna Ghufran Haroun Hamed Warasneh yar shekara 31 da haihuwa sojojin isra’ila sun harbeta da Bullet ne gefen hannunta na hagu.
READ MORE : Raisi; Iran Babbar Amintacciyar Abokiyar Tarayyar Nahiyar Africa Ce.
Kungiyar bada agaji ta red crescent ta falasdinu ta ce sojojin Isra’ila sun hana ma’aikatan lafiya su bata kulawa a lokacin da lamarin ya afku sanadiyar haka bayan minti 20 da afkuwar lamarin ta yi shahada.
READ MORE : Don shayar da yahudawan sahyoniyawan wuta su danne maruwaitan gaskiya.
READ MORE : Shugaban na Hamas ya taya kawancen kungiyar Hizbullah murna kan majalisar dokokin kasar Lebanon.