‘Yan tawayen yankin Tigray na Habasha sun zargi sojojin kasar da kaddamar da mabanbantan hare-hare ta kasa a kusan kowanne sashe na yankin ciki har da Amhara duk kuwa da lafawar rikicin da yankin ke gani tsawon watanni.
Duk da tarin zarge-zargen farmakin sojojin tare da take hakkin dan adama a yankin na Tigray har zuwa yanzu ofishin firaminista Abiy Ahmed bai tabbatar da hare-haren ba sai dai ya nanata kudirin gwamnatin na bayar da cikakkiyar kariya ga al’ummar kasar ga ‘yan tawayen.
Kungiyar ‘yan tawayen na Tigray na zargin firaminista Abiy Ahmad da kokarin sake mamaye yankin ta hanyar girke tarin motocin yaki da manyan makamai don kaluablantar mayakan ‘yan tawayen na TPLF da tuni gwamnatin kasar ta ayyana su a matsayin ‘yan tawaye.
Gwamnatin Abiy ta jaddada cewa ayyukan sojojin a arewacin kasar na kaiwa ‘yan tawaye hari, wanda a hukumance ta ayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda, babu gudu ba ja da baya.
A wani labarin na daban dakarun gwamnatin Habasha da wasu kungiyoyin yan kato da gora sun kaddamar da farmaki zuwa yankunan yan tawayen Tigray a yankin Amhara dake kan iyaka da fagen daga a arewacin wanna kasa.
Mai magan da yahun yan tawayen TPLF Getachew Reda dake fada da dakarun gwamnati tsawaon watanni 11 sun shirya wajen shiga yakin gadan-gadan.