Sojojin Faransa a Mali sun cafke kwamandan Kungiyar IS reshen kasashen yankin Sahel kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar.
Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin na Faransa ke shirin kammala janyewa baki daya daga Mali bayan sun shafe kusan shekaru 10 suna yaki da ayyukan ta’addanci a kasar.
Sojojin na Faransa sun dauki makwanni suna kitsa yadda za su kama kwamandan na IS akan iyakar Mali da Nijar.
Yanzu haka sojojin na Faransa za su yi wa Albakaye tambayoyi na tsawon kwanaki kafin daga bisani su mika shi ga hukumomin Mali don ci gaba da fuskantar tuhuma.
Wata majiyar tsaro da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, kiris ya rage ga Albakaye ya gaji kujerar tsohon shugaban IS a Sahel, wato Adnan Abu Walid al-Sahrawi wanda sojojin Faransa suka kashe shi a cikin watan Agustan bara.
Ana zargin Albakaye da cin zarafin fararen hula a kasashen Mali da Burkina Faso.
A wani labarin na dabn rikicin da ya barke a yankin Darfur na kasar Sudan tsakanin kungiyoyin Larabawa dasauran kabilu ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 100, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Hashem ya ce an kashe mutanen ne mafi yawa a tsakanin kabilar Gimir a lokacin arangamar, amma ba a bayyana adadin mutanen da aka kashe a cikin kabilar Larabawa ba.
Fadan dai ya barke ne a makon da ya gabata bayan wata takaddamar gonaki tsakanin mutane biyu da suka fito daga kabilun biyu..
A cikin watan Afrilu, sama da mutane 200 ne aka kashe a fadan da aka gwabza tsakanin kabilun Larabawa da na Gimir a yammacin Darfur.
Yankin Darfur dai ya kasance cikin yakin basasa a tsawon shekaru uku a lokacin mulkin shugaba Omar al-Bashir.
Yayin da wasu manyan kungiyoyin ‘yan tawaye suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 2020, har yanzu munanan tashe-tashen hankula na ci gaba da kamari kan rikicin filaye da dabbobi.