Wasu dakarun sojoji a kasar Gabon sun bayyana a gidan talabijin din kasar, inda suka bayyana cewa sun karbe mulki daga hannun gwamnatin farar hula a kasar.
Sun ce sun soke sakamakon zaben ranar Asabar da aka gudanar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Hukumar zaben ta ce Mista Bongo ya samu nasara ne a kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.
Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalansa suka yi a Gabon.
Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin a ranar Laraba, inda suka sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa “dukkan hukumomin kasar”.
Sun kuma ce sun rufe iyakokin kasar har sai illa masha Allah.
Source: LEADERSHIP HAUSA