Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan IPOB a Imo.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe wani mamba na kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a yankin Ihioma da ke karamar hukumar Orlu a jihar Imo da ke kudancin kasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi.
Ta kara da cewa dakarun nata sun kai farmaki kan mambobin kungiyar, sun kuma yi musayar wuta a wata hanya da ake kira Banana Junction, daya daga cikin yankunan da IOPB ta tilasta wa mutane su rika zaman- gida.
A musayar wutar ce suka yi nasarar kashe kwamandan IPOB din, lamarin da ya sanya sauran suka tsere.
Sojojin dai sun ci gaba da neman wadanda suka tsere da ke ta da zaune-tsaye da hana mazauna yankin sakat.
Sai dai rundunar sojin ta ce IPOB sun fara yada wani bidiyon farfaganda domin jama’a su tausaya musu, inda suka bukaci a yi watsi da shi.
READ MORE : Mali ta samu karin makaman soji daga Rasha.
Arangama tsakanin jami’an tsaron Najeriya da mambobin IPOB ba sabon abu ba ne, musamman a yankin kudancin kasar da suke kokarin ballewa da kafa Jamhuriyar Biafra.