Sojin Najeriya sun gano naira miliyan 60 da za a kai wa ‘yan fashin daji kudin fansa.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gano naira miliyan 60 da aka yi nufin kai wa ‘yan ta’adda kudin fansar karbo wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Jaridar PRNigeria da ke da alaka da jami’an tsaron Najeriya ta rawaito cewa sojin sun ce ana zargi a cikin wadanda aka samu da kai kudin fansar har da jami’an tsaron farin-kaya wato DSS.
Har wa yau, dakarun sun yi nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su da suka hada da mata da kananan yara.
Dakarun, wadanda suka hada da sojin sama da na kasa, sun kai ga cin karfin ‘yan bindigar. An gano muggan makamai da bindiga kirar AK47, da albarusai da sauransu.
Sojojin sun ce za su mika batun jami’an tsaron da suka hada da na DSS da ake zargi da kai kudin fansar ga ma’aikatar tsaron Najeriya, domin gudanar da bincike