Sojin Isra’ila Sun Sake Kashe Wani Bafalasdine.
Rahotanni daga falasdinu na cewa sojojin Isra’ila sun harbe har lahira wani bafalasdine a yammacin kogin Jordan.
A kwanan nan ana dai cikin zaman dar dar a yankunan Falasdinawa da Isra’ilar ta mamaye musamman a garin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da firaministan Isra’ila Naftali Bennett ya baiwa dukkan jami’an soji da na tsaro cikakken ‘yancin gudanar da ayyukansu a yankunan, furucin da ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta dauka a matsayin umarni na kashe Falasdinawa.
READ MORE : Siyar da makamai na Isra’ila ya kai dala biliyan 11.3 a cikin 2021 – 7% zuwa Tekun Fasha.
Game da halin da ake ciki a yankin MDD ta bakin Babban sakatarenta Antonio Guterres, ya nuna matukar damuwa game da halin da ake ciki na ruruwar wutar rikici tsakanin Faladina da Isra’ila.
READ MORE : Kamaru Da Amurka Sun ‘Keta’ ‘Yancin Masu Neman Mafaka: HRW.