Shugaban Sojin da suka gudanar da juyin mulki a kasar Guinea sun fara tattaunawa da bangarorin siyasar kasar na kwanaki 4 da ake saran ya bude kofar mayar da kasar mulkin farar hula.
Ana kuma saran sojojin su gana da shugabannin kungiyoyin fararen hula da jami’an diflomasiya da kungiyoyin kwadago tare da shugabannin kamfanonin ma’adinai.
A wani labarin na daban ayan juyin mulkin, shugaban sojin Laftanar Kanar Mamady Doumbouya ya zargin tsohuwar gwamnatin Conde da take hakkin ‘yan kasa, yayin da ya yi alkawarin kafa gwamnatin hadin kai wadda za ta jagoranci shirin mika mulki ga fararen hula.
Ana saran shugaban sojin ya yi jawabi ga jama’ar kasa bayan tattaunawar ta yau.
Tsohon Firaministan Guinea kuma jagoran ‘yan adawa, ya bukaci kungiyar ECOWAS da kada ta kakabawa kasar takunkumin karya tattalin arziki, saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a makon da ya gabata, matakin da ya bayyana a matsayin ci gaba ga kasar ta su.
Sojojin da ke mulkin Guinea na fuskantar matsin lambar diflomasiyya bayan da dakaruaa na musamman karkashin jagorancin Laftanar Kanal Mamady Doumbouya suka kwace mulki ranar Lahadin da ta gabata tare da cafke tsohon shugaba Alpha Conde.
A ranar Larabar da ta gabata ne kuma kungiyar ECOWAS ta dakatar da Guinea, yayin da a ranar Juma’a, kungiyar Tarayyar Afirka AU ta bi sahu.
Yanzu haka dai Kungiyar ECOWAS na dakon rahoton tawagar da ta tura Guinea kafin yanke hukunci kan yiwuwar kakabawa kasar takunkumin karya tattalin arziki.