Sojin Faransa da ke yaki da ta’addanci a yankin Sahel sun sanar da kisa wani gawurtaccen dan ta’adda da ke jagoranci kungiyar ISGS mai ikirarin jihadi a yammacin Afrika.
Majiyar tsaron Faransa ta ce dakarunta sun yi nasarar kisan Boura jagoran kungiyar ISGS ne a wani harin jirgi marar matuki lokacin da dan ta’addan ke tsaka da tafiya a kan babur mai kafa biyu.
Kungiyar IS dai ta dauki alhakin kisan jami’an agajin 6 wadanda faifan bidiyo ya nuno yadda aka yi musu yankan bayan da mayakan kungiyar suka kama su lokacin da su ke tsaka da ziyara a wani gandun daji a Nijar guda cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da hare-haren ta’addanci.
Kakakin dakarun sojin na Faransa Kanal Pascal Ianni ya bayyana cewa sun gano Boura ne a cikin bidiyon kisan jami’an agajin na watan Agusta.
A ranar 9 ga watan Agustan da ya gabata ne, ‘yan ta’addan suka yiwa jami’an agajin na Faransa 6 kisan gilla galibinsu ‘yan shekaru 26 zuwa 31 baya ga direbansu da kuma mai tsaron lafiyarsu lokacin da suke ziyara a gandun dajin Koure mai tazarar kilomita 60 daga Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.
A wani labarin na daban ‘Yan sanda a kasar Faransa sun ce akalla mutane sama da 50 aka kama a karshen mako lokacin da magoya bayan kasar Algeria suka gudanar da murnar nasarar da kasar ta samu wajen lashe kofin kwallon kafar kasashen Larabawa, kuma akasarin su an kama su ne kusa da fadar shugaban kasa.
Algeriya ta doke Tunisia da ci 2-0 a wasan karshe da aka kara a Qatar wajen lashe kofin, abinda ya sa magoya bayan kasar a biranen Faransa da suka hada da Paris da Lyon da kuma Roubaix suka fantsama tituna domin nuna murnar su.
Kasa da makonni uku kenan da Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya isa Algeria a wani yunkuri na gyara alakar kasashen biyu bayan sabanin da suka samu a baya-bayan nan wanda ya kai ga musayar janye jakadun juna.