Rundunar sojan ruwan Morocco ta ceto bakin haure 368 a makon da ya gabata ciki har da kananan yara uku yayin da suke kokarin tsallaka tekun Meditaraniya don isa kasar Spain.
Kamfanin dillacin labarai na MAP ya ruwaito cewa, bakin hauren, galibinsu sun fito daga yankin kudu da Saharar Afirka, an ceto su ne tsakanin ranakun Talata zuwa Juma’a lokacin da kan kanan kwale-kwalen roba dake dauke da su suka shiga cikin matsala.
Ko a makon da ya gabata, rahotanni suka ce sojan ruwan Morocco sun ceto bakin haure 344 a tekun Bahar Rum da Atlantic
A wani labarin mai kama da wannan ma’aikatar harkokin cikin gidan Spain ta sanar da maida ‘yan ci rani fiye da dubu 6 da 500 da suka ketara cikin kasar zuwa Morocco.
Bayanai sun ce hukumomin Morocco sun sun sassauta matakan tsaron dake kan iyakarsu da yankin Cueta na Spain a baya bayan nan, matakin da wasu masharhanta ke kallo a matsayin raddi ga gwamnatin Spain saboda karbar bakuncin jagoran masu fafutukar kafa kasar Plisario Brahim Ghali, wanda tun a watan jiya yaje kasar ta Spain domin duba lafiyarsa.
Sai dai yayin ganawa da manema labarai a jiya, ministan cikin gidan Spain Fernando Grande-Marlaska, ya bayyana fatan kawo karshen tsamin dangantakar da ta kunno kai tsakanin su da Morocco nan bada dadewa ba.
Ana dai fuskantar babbar matsalar ‘yan cirani masu saida rayuwa su fada kasashen turai domin samun mafaka da kuma samun sauyin rayuwa amma sai dai hakan yana tattare da manyan matsaloli wadanda suka hada da ta rayuwa, lafiya da kuma mutunci.
Masu cirani dai sukan haura kasashen Italiya, spain da sauran kasashen yammacin turai ta hanyar teku.