An dakatar da fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hollywood Will Smith daga halartar bukukuwan gasar Oscar na tsawon shekaru 10.
Shugabannin gasar karrama jaruman fina-finan ta Oscar kusan dubu 10 ne suka yi taro da safiyar jiya Juma’a don tattaunawa kan marin da Will Smith ya shararawa jarumin barkwanci Chris Rock.
Sai dai hukuncin na su bai soke kyautar gwarzon gasar ta Oscar da Smith ya samu a watan da ya gabata ba, saboda fim din da ya kasance tauraro a cikinsa wato “King Richard”.
Zalika ba a hana Will Smith tsayawa takarar gasar ta Oscar a nan gaba ba.
A cikin taƙaitaccen bayani kan hukuncin da ya hau kansa, Smith ya bayyana amincewa tare da mutunta matakin da aka dauka.
A wani labarin na daban Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar wakilan kasar daidaita kasafin kudi na matsakaicin zango don samar da Naira tiriliyan 4 da nufin sanya su a bangaren tallafin man fetur.
A cewar shugaban Najeriyar an ware Naira biliyan 442 ne kawai don tallafin man fetur a kasafin kudin shekarar bana ta 2022 daga Janairu zuwa Yuni, amma saboda tashin farashin danyen mai, da kuma dakatar da shirin cire tallafin man kwata kwata, kasar za ta bukaci karin Naira tiriliyan 3 da biliyan 557 domin ci gaba da biyan tallafin.
A ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta bayyana dakatar da shirinta na cire tallafin man fetur a shekarar bana ta 2022, matakin da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ce ba zai dore ba.