Siyasar Kano; Ganduje ya je kamun ƙafa gidan Shekarau.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara gidan tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, wanda rahotanni ke cewa yana daf da ficewa daga jam’iyyar.
Mai magana da yawun Malam Shekarau Sule Ya’u Sule, ya tabbatar wa BBC Hausa cewa cikin daren Juma’ar nan Shekarau ya karbi baƙuncin Ganduje, wanda ya je da zummar lallashi da kuma sauya wa Shekarau ra’ayi.
Ko da yake kakakin tsohon gwamnan ya ce zuwa yanzu basu san me mutanen biyu suka tattauna ba, ba za a iya haƙiƙance ko shekarau zai amince da sulhu da ɓangaren Ganduje ko bazai amince ba a wannan lokaci.
Rikici dai ya yi ƙamari tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Ganduje kan jagorancin jam’iyyar APC a jihar Kano, lamarin da ya kai ga har kotun ƙoli, daga bisani aka tabbatar da shugabancin jam’iyyar na ɓangaren Ganduje a matsayin halastacce.
An yi ta yaɗa rahotannin cewa tsohon gwamnan na Kano, Shekarau zai sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP ta Rabiu Musa Kwankwaso, kodayake Shekarau din bai bayyana haka da bakinsa ba.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama a Kano kamar tsohon mai ba wa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa Kawu Sumaila, da tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kabiru Alhassan Rurum da wasu yan majalisar dokokin jihar kusan 13 da na wakilai sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ta NNPP ta Kwankwaso.