Siriya; An Yi Kokarin Kishe Shugaban Asad Ba Tare Da Samun Nasara ba.
Kafafen yada labarai da dama sun bada labarin cewa wasu mutane wadanda ba’a bayyana sunayensu har yanzun ba, sun yi kokarin kashe shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad a dai dai lokacinda yake shiga masallacin Al-Hassan na birnin Damascus babban birnin kasar don halattar sallar idi a safiyar yau litinin.
Tashar talabijin ta AL-Manar ta kasar Lebanon ta bayyana cewa an yi sallar idi tare da shugaban ba tare da wata matsala ba. Amma wasu hotunan bidiyo da aka yada a kafafen sadarwa na zumunta sun nuna kokarin da wasu suka yi na kashe shugaban a lokacinda yak e kokarin shiga masallacin.
READ MORE : Bikin Ranar Ma’aikata Ta Duniya, 02 May 2022.
Har’ila yau matar shugaban Asma’u Asad ta bayyana cewa jami’an tsaron kasar zasu yi duk abinda zasu iya don kama wadanda suka yi wannan yunkurin wanda bai sami nasara ba. Gwamnatin kasar Siriya da jami’an tsaron kasar dai, har yanzin basu fadi kome dangane da yunkurin ba. Sai dai wasu kafafen yada labarai na kasar Siriya sun bayyana cewa babu gaskiya a cikin wannan labarin.
READ MORE : Mairupol – An Fara Kwashe Fararen Hula Daga Kamfanin Karafa.