Sinawa mazauna kasar Morocco, sun samar da tallafin kudade da sauran ababen bukata ga al’ummun kasar da ibtila’in girgizar kasa mai karfi ya auku, wadda kuma kawo yanzu ta haddasa rasuwar mutane kimanin 2,862.
Da yake tsokaci game da hakan, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Litinin, shugaban kungiyar Sinawa mamallaka kamfanoni da ‘yan kasuwa dake Morocco Lin Weiqiang, ya ce sun yi kira ga mambobin su da su samar da tallafi yadda ya kamata, kuma da zarar sun tattara, za su mika shi ga ofishin jakadancin Sin dake kasar.
Lin ya ce a halin yanzu ma, cibiyar bunkasa cinikayya ta Sin da Morocco ta fara mika kayayyakin agajin gaggawa zuwa yankunan da ibtila’in ya auku.
Tun a ranar Asabar din karshen makon jiya ne kungiyar Red Cross ta Sin, ta sanar da aniyar mika tallafin kudaden da suka kai dala 200,000 ga kungiyar agaji ta Morocco ko MRC, a matsayin agajin jin kai na gudanar da aikin ceto, da ayyukan rage radadin ibtila’in. (Mai fassara: Saminu Alhassan).
A wani labarin na daban mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labarai na yau da kullum yau Litinin din nan cewa, kasar Sin ta damu matuka da girgizar kasar da ta auku a kasar Morocco, kuma tana son ci gaba da taimakawa kasar Morocco bisa bukatunta.
Mao Ning ta bayyana cewa, a kokarin ganin an taimakawa kasar Morocco wajen tinkarar mummunan iftala’in girgizar kasar da ta afkawa kasar, kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta sanar da cewa, za ta baiwa kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Morocco taimakon gaggawa na tsabar kudi har dalar Amurka dubu 200.
Kana hukumar kula da harkokin hadin gwiwa da raya kasa ta duniya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a shirye take ta ba da agajin gaggawa bisa la’akari da bukatun wadanda lamarin ya shafa na Morocco.
Firaministan Sin Ya Gana Da Shugabar Hukumar EU Da Takwaransa Na Birtaniya
Kasar Sin tana son ci gaba da taimakawa Morocco bisa bukatunta.(Ibrahim)
Source: LEADERSHIPHAUSA