Hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta sanar a jiya Laraba cewa, Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya lashe zaben da kuri’u kimanin miliyan 8 da dubu 800, kasar sin tabi sahun masu taya murna.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ta bayyana a yau Alhamis cewa, bangaren Sin ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben.
An yi imani cewa, a karkashin jagorantar Tinubu, Nijeriya za ta samu manyan sabbin nasarori.
A gun taron manema labarai da aka saba yi Alhamis din nan, Mao Ning ta jadadda cewa, Nijeriya muhimmiyar abokiyar kasar Chana bisa manyan tsare-tsare ce a cikin nahiyar Afirka.
A cikin ‘yan shekarun nan, alakar dake tsakanin Sin da Nijeriya ta bunkasa cikin sauri, kana hadin gwiwa a fannoni daban daban, ya haifar da sakamako mai kyau, wadanda suka kawo alheri ga al’ummar kasashen biyu.
Kasar Chana tana son yin aiki kafada da kafada da sabuwar gwamnatin Nijeriya, wajen karfafa mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, ta yadda za a ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Najeriya zuwa wani sabon matsayi.(Safiyah Ma).
A wani labarin na daban a ranakun 4 da 5 ga watan Maris na bana, za a gudanar da tarukan kasa guda biyu a nan kasar Sin, wato cikakken zama karo na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin karo na 14, da kuma cikakken zama karo na farko na babban taron wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 bi da bi.
Ajandar babban taron wakilan jama’ar kasar Sin na wannan karo, shi ne duba rahoto game da yadda gwamnatin kasar Sin ta sauke nauyin dake biya wuyanta a bara, da aikin da za ta yi a bana.
Sannan wakilan jama’a za su duba rahoto kan yadda aka aiwatar da shirin raya tattalin arzikin kasa da ci gaban jama’a na shekarar 2022 da daftarin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar kasa na shekarar 2023, da daftarin tattalin arzikin kasa na shekarar 2023, da shirin ci gaban zamantakewa, da kuma nazarin tsarin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma, da duba rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’a, duba rahoton aiki na kotun koli, duba rahoton aiki na majalisar koli ta jama’a, zabe da kuma nada sabbin jami’an hukumomin gwamnatin kasar Sin, kamar su firaministan gwamnatin kasar, da mataimakansa da ministocin gwamnati, da dai sauransu.
Ajandar taron kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin shi ne saurara da duba rahoton ayyukan zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, da rahoton ayyukan shawarwari, dubawa da zartas da gyaran kundin sauraran shawarwari na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, ya kuma zabi shugaba da mataimakansa da babban sakatare da mambobin zaunanen kwamitin na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin karo na 14 da dai sauransu.
Akwai sabbin abubuwa da yawa a cikin tarukan kasa guda biyu na wannan karo, wanda ke jan hankalin jama’a a duk fadin kasar. A siyasance, sabbin wakilan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da mambobin kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin za su halarci tarukan biyu.
A lokacin, wakilai da ’yan kwamiti daga wuraren kasar daban daban za su gudanar da ayyukansu, kana za su tuntubi juna da ba da shawarwarinsu.
A sa’i daya kuma, yayin da aka fitar da jerin sunayen “manyan shugabanni” da tawagogin jagoranci na cibiyoyi daban daban, fagen siyasar kasar Sin zai kammala mika mulki tare da kafa wani sabon layi.
Kamar yadda aka saba, sabon firaministan kasar Sin da mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin, za su fito fili don ganawa da ‘yan jaridun kasar Sin da na kasashen waje.
A madadin sabuwar gwamnatin tsakiya, sabon firaministan zai amsa tambayoyi daga manema labarai, da gabatar da manufofin da kuma mayar da martani ga tsammanin jama’a.
Ta fuskar tattalin arziki, yadda za a tsara ingantaccen ci gaba a cikin rahoton ayyukan gwamnati na wannan shekara, musamman ma abin da aka sa a gaba ga tattalin arzikin kasar a shekarar 2023, ya cancanci a ci gaba da kula da su.
A game da rayuwar jama’a, sabon kwamitin wakilan zai tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa da rayuwar jama’a, da tabbatar da burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa a hakika, da rubuta wani sabon labari game da dimokradiyyar kasar Sin.
A fannin yin gyare gyare da bude kofa ga waje, bana shekara ce ta cika shekaraku 45 da gudanar da manufar yin gyare gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ta kasar Sin, kana sabbin matakan gyare gyare da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin ta dauka sun jawo hankalin duniya baki daya.
Wadanne irin matakan bude ido ne majalisar wakilan jama’ar kasar za ta dauka a bana cike da fata?
Ta fuskar diflomasiyya, shugaban kasar Philippines, da shugaban Turkmenistan, da firaministan Kambodia, da shugaban kasar Iran sun ziyarci kasar Sin cikin nasara, dangantakar diflomasiyya tsakanin shugabannin kasa da kasa ta fara shiga wani sabon matsayi a farkon wannan shekara.
Shekarar bana ta zo daidai da cika shekaru 10 da gudanar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kuma yadda kasar Sin za ta ba da labarin hadin gwiwa kan “berin raya kasa” da “hanyar farin ciki” a harkokin diflomasiyyar cikin gida shi ma zai jawo hankalin jama’a.
Bugu da kari, wannan shekara ita ce karon farko da sabon ministan harkokin wajen kasar Sin zai bayyana a tarukan biyu bayan kama aiki.
Ta hanyar lura da taron manema labarai na ministan harkokin wajen kasar, kasashen waje na iya samun dan karamin ilimi da karin haske kan sabbin hanyoyin da ake bi na diflomasiyyar manyan kasashe.
Source:Leadershiphausa