Wata ƴar jarida ta ƙasar Masar, Siham Shamalakh ta shaida wa kafar yada labaran Turkiyya irin bala’in da ta shiga sakamakon yaƙin Gaza da yadda ta bar mijinta a Gaza domin zuwa wurin ƴaƴanta waɗanda suka yi gaba zuwa Masar domin gudun hijira.
Bayan jira cikin tsammani na kusan watanni biyar, lokacin ya zo a ƙarshen watan Janairu: wato damar barin Gaza domin tsere wa mugun yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar a birninmu da ta mamaye.
Siham tace don jin daɗin kaina da mijina, wani Bafalasɗine ɗan uwana da ke gudun hijira wanda muke zaune a Rafah ya bayyana cewa a ƙarshe sunana ya bayyana a cikin jerin waɗanda za a kwashe a ranar 26 ga Janairu.
Ni asalin ƴar Masar ce, amma mijina ba ɗan Masar bane.
“Ki shirya, dole ne ki kasance a mashigar Rafah gobe da misalin bakwai na safe,” kamar yadda Abu Shaaban ya shaida mata cikin murmushi.
Shi da ni mun jira tsawon lokaci domin zuwa wurin ƴaƴana, waɗanda suka yi ƙoƙarin tserewa zuwa Masar tare da yayata a watan Disamba.
Zuwa watan Janairu, lamarin ya ƙara ƙazancewa a Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ta ƙara tura sojojinta kan farar hula inda suka kashe dubban Falasɗinawa.
Yadda tafiyata ta zama zahiri ya samo asali ne bayan ɗana Khaled ya yi ƙoƙarin kirana a waya daga Masar bayan ya yi yunƙurin hakan sau da dama.
Sai dai murna da shauƙi sun lulluɓe ni – duk da ina tunanin tafiya, sai dai na shiga damuwa domin na gano cewa sunan mijina ba ya cikin waɗanda ke shirin tafiya.
Duk da zuciyata ta yi nauyi, amma sai da na tafi na bar shi, inda na yi ta ƙoƙarin neman yadda iyalinmu za su ƙara haɗuwa tattare.
Sai dai na ƙara shiga damuwa bayan na yi tunanin cewa ba lallai ne na rinƙa samunsa yadda nake so a waya a kullum ba.
Tun bayan soma yaƙin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, hare-haren Isra’ila sun yi mummunan tasiri kan kayayyakin sadarwa na Gaza, wanda hakan ya rinƙa jawo ɗaukewar sabis ɗin waya.
Falasɗinawan da ke Gaza na ci gaba da fama da matsalolin intanet da na wayoyin sadarwa.
Sai dai tafiya ba tare da mijina ba, Ahed, bai kasance lamari mai sauƙi ba; ya karya mani zuciya ya barni cikin fargaba.
Na shafe dare ina ta tunani kan matakin da zan ɗauka, har sai da na yi tunanin tsayawa tare da shi. Duk da damuwar da nake da ita game da ƴaƴana, amma na kasa tunanin barin Ahed a baya domin ya fuskanci abin da ba shi da tabbaci a Gaza shi kaɗai.
Birnin Rafah da ake zargin sojojin Isra’ila sun ayyana shi a matsayin wuri mai aminci ga fararen hula, yana fuskantar barazanar ayyukan sojin Isra’ila a kullum.
“Kada ki yi tunanin wani abu, na ji muku daɗi ke da ƴaƴana, zan kasance cikin aminci, kada ki damu,” kamar yadda Ahed ya shaida mani.
Mun rungume juna inda na rinƙa kuka. Cikin dare, na haɗa jakata sannan na yi bacci na tsawon sa’o’i sannan na tashi da misalin biyar na asuba.
Na sha wahala domin ban samu motar tasi wadda za ta kai ni iyakar Rafah ba saboda ƙarancin man fetur.
Makwabcinmu ne wanda yake da mota ya tuƙa mu zuwa can inda muka biya shi shekel 250, kimanin dalar Amurka 68 kenan.
Yayin da muka kama hanya, sai na kalli teku da kuma mutanen da ke kusa da ni. Zuciyata ta yi nauyi domin na ji ba lallai ne na iya komawa Gaza nan kusa ba sakamakon babu wata alamar kawo ƙarshen yaƙin nan kusa.
Yayin da nake bankwana da abubuwan da na sani a gefen teku da tituna, na zura ido kan tantuna da yadda jama’a suka taru. Lokaci ne mai raɗaɗi, wanda ke nuna bankwana na ƙarshe ga yanayin bakin ciki na Gaza.
A daidai lokacin da na kawo mashigar Rafah, sai na ga ɗumin jama’ar da suka taru a wurin, wanda wannan tuni ne kan irin hijirar da ake yi sakamakon zaluncin da Isra’ila ke aikatawa.
“Da alama duka ƴan Gaza na guduwa,” kamar yadda na shaida wa kaina. A farko na yi tunanin ba alama ce mai kyau ba, amma a daidai lokacin, amma a gaskiya ya kamata a gudu daga kisan kiyashin da ake aikatawa.
A kusa da mashigar, wasu mutane sun kafa tenti, inda wasu da dama kuma bacci ya ɗauke su a kan kujerunsu, inda suke jiran a kira sunayensu domin su kama hanya.
A daidai lokacin da nake lura da gefena da idanuwana na ƴar jarida, duk wani bayani ya kasance lamari mai ban mamaki a gare ni; mashigar ta yi kama da wani sansani fiye da iyakar da take.
Abin da nake jira ya iso bayan na ji wani ma’aikaci ya kira sunana a mashigar. Bayan na cika da shauƙi, sai na rungume mijina sosai kafin na shiga wurin tafiyar.
Sai na buƙaci Ahed ya jira mu na awa ɗaya, inda nake tunanin zan iya magana da wani jami’i da ke ciki ya bar shi domin mu taho tare, sai dai jami’in ya ƙi amincewa.
“Idan sunansa ba ya kan jerin sunayen, ba zai iya tafiya ba…kuma kar ki ɓata mani lokaci.”
Sai na tafi zuciyata cikin nauyi. Bayan an buga mani hatimi kan fasfo ɗina, sai na shiga mota zuwa gefen Masar da ke mashigar Rafah.
Duba Nan: Yemen Na Fafatawa Da Amurka Da Ingila
An yi wa kowane matafiyi cikakken bincike na tsaro, inda jami’an na Masar suke bin diddiƙin hatimin tafiya da da sunaye a lokacin binciken tare da ɗaukar bidiyon fasinjojin da kemara – wanda lamari ne da ban san da shi ba, amma ya kasance dole ga wannan tafiyar zuwa Masar.