Shugabannin Kasashen Rasha, Turkiyya Da Iran, Zasuyi Taro Kan Siriya A Tehran.
Shugabannin kasashen Rasha da Turkiyya da kuma Iran, zasu gudanar da wani taro game da batun Siriya a ranar Talata mai zuwa.
Fadar shugaban Rasha ta Kremlin, ta sanar cewa yayin taron shugabannin kasashen uku Vladimir Putin, da Recep Tayyip Erdogan, da kuma Ibrahim Ra’isi, zasu tattaunawa kan Siriya da kuma alakokin dake a tsakankaninsu.
Kakakin fadar Kremlin, Dmitri Peskov, ya bayyana wa manema labarai cewa ana shirya ziyarar da shugaban kasar Vladimir Putin zai kai a Tehran inda zai halarci taron na ranar 19 ga watan Yulin nan.
Iran ma ta bakin shugaban kwamitin tattalin arziki na majalisar dokokin kasar ta tabbatar da shirin ziyarar ta shugaba Putin, dake zuwa bayan wacce takwaransa na Iran din ya kai kwana bayan domin karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
Haduwar
READ MORE : Biden ba zai iya magance kiyayyar da aka yi wa gwamnatin sahyoniya da tafiya guda ba.
za ta kasance irinta ta farko ta tsakanin shugabannin uku tun bayan zuwan
sabuwar gwamnatin Shugaba Ra’asi na Iran.
READ MORE : Yadda ‘Yan ta’adda suka kula da mu inji Fasinjan Jirgin Abuja-Kaduna da ya kubuta.
READ MORE : NDLEA : An yi ram da daya daga cikin wadanda suka tsere daga kurkukun Kuje.