Shugabannin Kasashen Mali Da Burkina Faso Sun Gana A karon Farko A Bamako.
Shuwagabannin sojoji na kasashen Mali da Burkina Faso sun gana a birnin Bamako babban birnin kasar Mali a karon farko tun bayan juyin mulkin da suka jagoranta a kasashen nasu.
Shafin yanar gizo na labarai Africanews ya bayyana cewa Kanar Assimi Goita shugaban gwamnatin sojoji na kasar Mali ya gana da tokwaransa na kasar Burkina faso Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a birnin Bamako a ranar Asabar da ta gabata, inda bangarorin biyu suka tattauna batuituwan da suka shafi kasashen biyu, musamman matsalolin tsaro da suka addabar kasashen biyu.
A jawabin da ya gabatar bayan isarsa beinin Bamako Paul-Henri Sandaogo Damiba ya ce ya zo kasar Mali don ganawa da jami’an gwamnatin kasar kan matsalolin da kasashen biyu suke fuskanta, musamman ta tsaro. A nan akwai bukatar a kara karfafa dangantakar tsaro dake tsakanin kasashen biyu, don magance matsalolin tsaron da mutanemmu suke fama da su.
Ziyarar da Paul-Henri Sandaogo Damiba ya kai kasar Mali dai ya zo dai dai lokacinda gwamnatin kasar ta Mali ta sake sojoji 3 daga cikin sojojin kasar 49 na kasar Ivory Coasta wadanda tave sun shiga kasar ba tare da izini ba.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa shugaba Paul-Henri Sandaogo Damiba. Ya wace zuwa kasar Ivory Coast bayan ya kammala ziyara a kasar ta Mali.