Shugabannin Faransa da Jamus sun sake shiga tsakani kan rikicin Rasha da Ukraine.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz sun tattauna da shugaban Rasha Vladimir Putin, da na Ukraine Volodymyr Zelensky, daya bayan daya, don sake shiga tsakani kan rikicin kasashen Rasha da Ukraine.
A yayin tattaunawar da aka yi, shugaba Putin na Rasha, ya bai wa Macron da Scholz cikakken bayani kan jerin shawarwarin da aka yi ta kafar bidiyo a baya-bayan nan tsakanin wakilan Rasha da na Ukraine, da kuma ainihin halin da ake ciki na jin kai.
M. Putun, ya ce bangaren Ukraine ya yi matukar karya dokar jin kai ta kasa da kasa, kamar jibge manyan makamai a kusa da wuraren zama, da asibitoci, da makarantu, da gidajen renon yara da sauransu.
A wannan rana kuma, fadar Elysee ta shugaban kasar Faransa, ta fadawa kafafen yada labaran kasar cewa, Faransa da Jamus sun bukaci Rasha ta kawo karshen harin da ake kai wa Mariupol na Ukraine, saidai Putin din bai nuna ra’ayin tsagaita bude wuta ba, don haka Faransa ta yanke shawarar sanyawa Rasha sabbin takunkumai.