Sakamakon fitar da wasu mahimman takardu Shugabannin Duniya Sun Mayar Da Martani ‘Pandora Papers’da ke bayyana yadda dimbim fitattun mutane a duniya suka boye tarin dukiyoyi da suka kai miliyoyin Dala a asusun ajiyar kasashen ketare da babu haraji, gwamnatoci sun yunkuro don rage tasirin wannan tonon sililin na binciken da aka yi wa lakabi da ‘Pandora Papers’.
Cikin wadanda sunayensu suka bayyana a wandannan kundaye ,akwai tsohon Fiiraministan Birtaniya, wanda aka nuna ya kauce wa biyan harajin kan wani gidansa na birnin Landan.
Babu sunan shugaban Rasha Vladimir Putin, amma kuma an danganta shi da wasu kadarori na makusantan sa a birnin Monaco na Faransa, musamman wani gida na kusa da teku, mallakin wata mata da suka haihu da ita.
Sai dai kakakin fadar Kremlin ta Rasha, Dmitry Peskov ya ce, zargi ne mara tushi.
Ita ma Jordan ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin watsi da rahoton cewa ,an bankado tarin kadarori da suka kai miliyan 100 na Dala da Sarki Abdallah na biyu ya tara a California da Landan.
Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa ta gudanar da wannan bincike da akayi wa lakabi da ‘Pandora Papers’ , wanda kafofin yada labarai da suka hada da Washington Post, BBC da Guardian suka watsa.