Shugabannin Africa Sun Bukaci Kudade Domin Yaki Da Canjin Yanayi.
Wakilai daga kasashen Afirca, sun bukaci kasashen da suka ci gaba da su cika alkawuran da suka dauka na kudi don taimakawa nahiyar wajen cimma burin da aka sanya a gaba na yaki da canjin yanayi gabanin taron Majalisar Dinkin Duniya na COP27 da aka shirya gudanarwa a Masar a cikin watan Nuwamba mai zuwa.
“Muna kira ga kasashen da suka ci gaba da su cika alkawuran da suka dauka na kudurorin sauyin yanayi da raya kasa, da kuma cika alkawuran da suka dauka na rubanya kudade don cimma sauyin da ake bukata, musamman ga Afirca,” in ji shugabannin na Afirca a birnin Alkahira, yayin taron share fage kan sauyin yanayi.
Jakadan Amurka kan sauyin yanayi John Kerry ya fadawa wakilan kasashen Afirca a ranar Laraba cewa yana fatan COP27 za ta iya sakin “makamashin da muke bukata don sauya duniya”, ” saboda muna cikin matsala”, in ji shi.
READ MORE : Benin Na Tattaunawa Da Rwanda Domin Yaki Da Ta’addanci.
Wannan taro na kwanaki uku da Masar ta karbi bakunci, ya gudana ne bayan wani taron koli da aka gudanar a ranar litinin a kasar Holand, da nufin tallafa wa Afirca ta fuskar sauyin yanayi.