Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da shirin musayar mukaman shugabancin ta yadda wadanda ke arewa zasu koma kudu, yayin da wadanda ke kudu zasu koma arewa.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai da shugaban gwamnaonin APC Atiku Bagudu suka bayyana wannan sabon tsarin bayan wani taron da suka gudanar tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake Abuja.
El Rufai yace taron na su wanda ya kunshi daukacin gwamnonin jam’iyyar ta su da shugaban kasa ya amince a mayar da daukacin kujerun dake arewacin Najeriya zuwa kudu, yayin da na kudu kuma zasu koma a rewa.
Gwamnan yace a karkashin wannan tsari, zasu koma shiyoyin su domin fasalta yadda zasu raba mukaman yadda kowanne bangaren na kasar zai samu wani mukami.
Ana saran jam’iyyar ta gudanar da tarukkan shiya da kuma na kasa a watan gobe.
Wannan taro bai ce komai ba dangane da inda shugaban kasa zai fito amma ga alama, yana iya komawa kudancin Najeriya tunda jam’iyyar ta kai kujerar shugabancin ta zuwa arewa.