Shugaban Rasha Viladmir Putin Zai kawo ziyara Kasar Iran A Mako Mai Zuwa.
Shugaban kwamitin tattalin arziki a majalisar shawara ta kasar Iran Mohammad reza Pourabarahimi shi ne ya fitar da wannan sanarwa , yana mai cewa shugaban na Rasha zai gana da shugaban babban banki Iran kumam za su rattaba hannun kan yarjeniyoyi guda biyu da suka shafi harkokin kudi.
Har ila yau ya kara da cewa shirin bunkasa hulda tattalin arziki tsakanin Iran da rasha shi ne zai kasance a sahun gaba a tattaunawar da za’a yi tsakanin shuwagabannin kasashen guda biyu.
Yace bukatar da rasha take da shi na bunkasa hulda tattalin arziki da kasar iran a halin yanzu ya karu fiye da kowanne lokaci a baya, kuma ana fatan ziyarar ta Putin za ta haifar da wannan yanayi mai kyau da yin aiki tare tsakanin kasashen Iran da Rasha.
READ MORE : Joe Biden Na Kokarin Taimakawa Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Ziarar Sa Zuwa Saudiyy.
Daga karshe ya nuna cewa takunkumin da kasahen Amurka da na turi suka kakabawa kasar Rasha ya sa take tsananin bukatar ganin ta kara karfafa dangantakar tattalin arziki dake tsakaninta da Iran.
READ MORE : Iran; Amurka Ba Zata Dorawa Kasar Ra’yinta Tare Da Zarge-Zarge, Ko Takunkumi Ba.